Kalaman soyayya masu dadi da ratsa zukata

Kalaman soyayya masu dadi da ratsa zukata

Ina godiya ga Allah daya bani kai amatsayin masoyina, me kaunata, cikar burina ,Wanda nake fata yazama miji agareni, kyaukyawar zuciyarkace ta bayyana kyawawan halayyarka wanda suke sakamin cikkakiyar nutsuwa acikin ruhina,sama cike take da taurari masu hasken dake haska duniya acikin kowani dare, Amma haske mafi haska fuska dake acikin duhun zuciya na ganshine acikin idanunka ka kukalamin dakanka, ina sonka,

 kasantuwarmu araye cikin ruhi guda daya yasanya zuciyoyinmu bugawa cikin lokuta makamantan juna.

Komai namu ya kasance yana  faruwa ne a lokaci guda hatta farin ciki dakuma bakin ciki wato ruhi daya gangar jiki kuma biyu farin ciki ka shine nawa.

Tabbas ubangijna ya cancanci yabo ta ko wace fuska bayan i imar rayuwa da ta lafiya da yayi mana se kuma ya kara mana da baiwar kasantuwa sanyin idanunmu acikinmu, wadda meke kalla muji nutsuwa ta sauka a jikinmu, hakika zan kula dakai kamar yadda zan kula da lafaiyar jikina,kuma insha Allah zan zama mai kyautatawa, faran tawa,da kuma ebema kewa akoda yaushe.

www.haskenews.com.ng

Related

Stay on op - Ge the daily news in your inbox